Labarai
Ina goyon bayan binciken da gwamnati ke yi akan mahaifana-Abdulaziz Ganduje
Dan Ganduje Ya Kai Ziyarar nuna goyon baya ga Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Na Kano, inda ya yaba bisa yadda gwamnati ke binciken Mahaifinsa.
Abdulazeez Ganduje, babban ɗan shugaban jam’iyyar APC da aka dakatar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai wa shugaban hukumar korafe-korafen da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin gado ziyara a ofishin sa.
Abdulazeez ya ziyarci Barrista Muhyi Rimin gado a yammacin Laraba domin nuna goyon bayansa ga yunkurin sa na yaki da cin hanci da rashawa.
Ya kuma bayyana amincewar sa da tuhume-tuhumen da hukumar take yi wa mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma dan uwansa.
Abdulazeez ya bayyana damuwarsa ga shugaban hukumar bisa rashin adalci da aka cire shi daga mukamin darakta na daya daga cikin kamfanonin da ake shari’a, inda ya nuna damuwarsa kan yadda aka kore shi ba tare da wani laifi ba.
A watan Satumbar 2021, Abdulazeez ya kai ƙara ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) kan mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje, inda ya zarge ta da cin hanci da rashawa.
A baya dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta dauki matakin shari’a kan Ganduje, da matarsa, Hafsat Umar, da dansa Umar Abdullahi Umar, da wasu mutane biyar bisa zargin almundahana, da karkatar da kudade da suka kai biliyoyin naira. Sauran mutanen da lamarin ya shafa sun haɗa da Abubakar Bawuro, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Limited.
You must be logged in to post a comment Login