Connect with us

Labarai

INEC: ba zata amince da shaida ko daya a kotun sauraron zaben shugaban kasa

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC  ta ce ba za ta gayyaci shaida ko daya ba don kare ta a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da ya gabata, wanda PDP da dan takararta Atiku Abubakar ke kalubalantar sakamakon.

PDP da Atiku Abubakar suna kalubalantar sakamakon zaben shugaban da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabarairun da ya gabata, wanda INEC ta ayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe.

PDP da Atiku Abubakar sun gabatar da shaidu guda 62.

Alkalin Kotun Justice Muhammad Garba ya bad a umarnin ci gaba da sauraron karar a yau Litinin, to amma Lauyan Buhari da APC Wole Olanipekun ya roki kotun ta ba shi damar gabatar da jawabi a gobe talata da karfe 2 na rana.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,394 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!