Labarai
INEC Kano:Shugaba Buhari ya samu nasara da kananan hukumomi 23
Bayan da aka sanar da sakamakon zabukan shugaban kasa dana ‘yan majalisun dokokin tarayya anan Kano, rahotanni daga hukumar zabe ta kasa (INEC), na nuna cewa shugaban Muhammadu Buhari ya zuwa yanzu ya samu nasara a kananan hukumomi ashirin da uku da aka fitar da sakamakonsu.
Haka kuma sakamakon ya nuna cewa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya yi rashin nasara a dukkannin kananan hukumonin da aka sanar a sakamakon zabukansu.
Jam’iyyar APC da dantakarar ta Muhammadu Buhari, ya samu jimillan kuri’u dubu dari shida da dubu goma sha uku da goma sha hudu.
Yayin da anashi bangaren Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu dari da tamanin da takwas da dari bakwai da talatin da biyu.
Haka kazalika shugaban hukumar zabe ta kasa INEC a nan Kano Farfesa Risqua Shehu, ya ce, za a sake gudanar da zabuka a wasu rumfunar zabe guda hudu a yankin karamar hukumar Dawakin Tofa.
Sai dai hukumar zabe ta kasa INEC ta ki amincewa da sakamakon zaben wata mazaba da ke yankin karamar hukumar Sumaila sakamakon gudanar da zaben ba bisa kai’ida ba, da kuma barazana ga jami’an hukumar zabe