Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Masu sanya ido na ECOWAS sun bukaci yan takarar shugabancin Najeriya su amince da sakamakon zaben

Published

on

Masu sanya idanu na kasashen yammacin Afurka ECOWAS sun bukaci ‘yan takarar shugaban kasa a Najeriya da su amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar da ta gabata, a duk yadda ya zo musu.

Shugaban tawagar kungiyar ta ECOWAS kuma tsohuwar shugaban kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ce ta yi wannan kiran yayin da ta ke bayyana sakamakon ayyukan kungiyar na wucin gadi jiya Lahadi a Abuja.

Ta ce kamata yayi bayan sanar da sakamakon zaben duk wanda ya ke da korafi ya garzaya kotu domin shigar da korafin sa.

Tsohuwar shugaban kasar ta Liberia ta kuma bukaci hukumar zabe ta kasa INEC da sauran masu ruwa da tsaki da su bi lamarin tattara sakamakon zaben cikin hanyoyin da suka da ce. Shugabar kungiyar masu sa idanun ta kungiyar ECOWAS ta kuma bukaci hukumar zabe ta kasa INEC da ta gudanar da gyare-gyare kan matsaloli da aka samu wajen gudanar da zabuka na nan gaba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!