Connect with us

Kiwon Lafiya

INEC:za ta yi jinkirin baiwa wanda ya samu nasarar zaben gwamnan jihar Zamfara

Published

on

Hukumar zabe ta kasa (INEC), ta ce za ta yi jinkirin baiwa wanda ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Zamfara da aka kammala a baya-bayan nan, takardar shaidar lashe zabe.

Haka zalika hukumar INEC ta kuma ce za ta yi jinkirin baiwa ‘ya’yan jam’iyyar ta APC da suka samu nasara a yayin zaben ‘yan majalisun dokokin jihar da aka gudanar a ranar tara ga watan da muke ciki na Maris takardar su ta lasisi.

Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na facebook.

A cewar sanarwar hakan ya faru ne sakamakon karbar takardar kotu wanda rushe zaben fidda gwani da jam’iyyar APC a gudanar a jihar.

A shekaran jiya litinin ne dai kotun daukaka kara da ke Sokoto ta rushe zabukan fidda gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar ta Zamfara.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!