Connect with us

Kiwon Lafiya

Diyar ga mataimakin shugaban kungiyar editoci ta kasa ta shake iskar ‘yanci

Published

on

Hajiya Habiba Abdulsalam wacce ‘ya ce ga mataimakin shugaban kungiyar Editoci ta kasa Malam Suleman  Uba-Gaya wacce aka sace a kwanakin baya anan Kano, ta shaki iskar ‘yanci, kuma tuni aka sada ta da iyalan ta.

Da yake shedawa manema labarai kan mumunan labarin Alhaji Uba-Gaya ya ce ‘yar ta sa ta gudu daga hannun wadanda suka sace ta a daren ranar Asabar.

Mataimakin shugaban kungiyar Editoci ta kasan ya kara da cewar, masu satar mutanen sun sace ‘yar ta sa ne ranar Juma’a tsakanin  karfe 5 zuwa 6 na yammacin ranar.

A cewar Malam Suleman Uba-Gaya Dan Uwan Habiba ne ya kira wayar ta bayan da ya kasa samu ta kuma ki shiga, daga nan ne suka shiga nema, yayin da mintuna kadan bayan da tayi Magana da daya daga cikin ‘yan uwan ta, hakan ne ya sababa cewa wasu da ba’a san ko suwaye ba sun sace ta.

Mataimakin shugaban kungiyar Editoci ta kasa ya kara da cewar yana godewa jami’an ‘yan sanda da hukumomin tsaro, saboda namijin kokarin da suka yi wajen ceto ‘yar ta sa a hannun masu satar mutane.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,742 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!