Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Barka Da Hantsi

Inganta ilimi: Za mu ginawa ma’aikata gidaje a ƙananan hukumomin su – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta gidaje dubu 10 ga ma’aikata a faɗin jihar.

Kwamishinan sufuri Mahmud Muhammad Santsi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio.

Santsi ya ce “Tuni gwamnati ta samar da filayen da za a ginawa ma’aikata gidaje don samar musu da sauki wajen zuwa guraren ayyukan su musamman ma malamai”.

Ya ƙara da cewa, a kowacce ƙaramar hukuma za a gina gidaje 100 da za’a fara da ƙananan hukumomi guda bakwai 7.

“Gwamnan kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sahalewa wannan ma’aikata domin siyo motoci masu ɗaukar mutane hamsin da shida 56 guda ɗari 100 don sauƙaƙa sufuri a Kano.

Mahmud Muhammad Santsi ya ce, nan ba da daɗewa ba matsalar cinkoson ababen hawa a jihar Kano za ta zama tarihi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!