Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jagoran ‘yan adawa a kasar Chadi ya zargi jami’an tsaro da yiwa iyalansa kisan gilla

Published

on

Daya daga cikin jagororin ‘yan adawa a kasar Chadi ya zargi jami’an tsaro da kisan gilla ga iyalansa a birnin Ndjamena.

Yaya Diallo wanda tsohon madugun ‘yan tawaye ne ya ce jami’an tsaron sun kai harin ne a gidansa da ke birnin N’Djamena babban birnin kasar.

A zantawa da manema labarai Yaya Diallo wanda ke neman takarar shugabancin kasar ya ce lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 28 ga watan Fabrairun  shekarar 2021.

Haka zalika ya kuma zargi dakarun da ke kula da fadar shugaban kasa karkashin jagorancin daya daga cikin ‘ya’yan shugaba Idriss Deby da laifin kisan gillar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!