Kasuwanci
Jakuna da babura ake amfani da su wajen safarar makamai a kan iyaka–Kwastam
Shugaban hukumar yaki da fasakwauri ta kasa (kwastam) kanal Hamid Ali mai ritaya, ya ce, masu safarar makamai ga ‘yan ta’adda ta kan iyakokin kasar nan da ke kan tudu, a yanzu sun fitar da wani sabon salo wajen amfani da jakuna da babura suna safafar makamai da su.
Kanal Hamid Ali mai ritaya, ya ce, batagarin suna hada baki da al’ummomin garuruwan da ke daf da iyakokin kasar nan wajen safarar makamai.
Shugaban hukumar ta kwastam ya bayyana hakan ne lokacin da ya gurfana gaban kwamitin kula da hukumar yaki da fasakwauri ta kasa (kwastam) ta majalisar wakilai.
Ya ce, abin haushin shine al’ummomin da ke rayuwa kusa da kan iyakokin kasar nan suna nuna alamun basa da masaniyar cewa yin fasakwaurin kayayyaki zuwa kasar nan haramun ne.
Kanal Hamid Ali mai ritaya ya kuma ce, hukumar tana aiki tukuru wajen ganin ta rage yadda ake safarar motoci da basu da inganci zuwa kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login