Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

JAMB yayi zargi kan zanga zangar adawa da ayyukan hukumar

Published

on

Shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB Farfesa Is-haq Oloyede yayi zargin daukar nauyin zanga-zangar adawa da ayyukan da hukumar ke aiwatarwa.

Is-haq Oloyede ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai yau a birnin tarayya Abuja, tare da bayyana sunan wani dalibi da hukumar ta kwce sakamakon jarrabawar sa mai suna Kokowa Cletus, bayan da aka same shi da laifin yunkurin shiga rumbun adana bayana hukumar domin kara adadin makin da ya samu tun farko.

Idan za’a iya tunawa a ranar ashirin da hudu ga watan da ya gabata na Yuni ne hukumar ta fitar da sunan wata daliba mai suna Adah Eche, da ake zargi da yunkurin karawa kanta makin sakamakon jarrabawar da ta rubuta a bana.

Shugaban hukumar ta JAMB yayi All— wadai da yunkurin shirya zanga-zangar adawa da ayyukan ta, tare da cewa abin takaici ne ace duk da irin ayyukan da take yi wajen inganta harkokin karatun dalibai a kasar nan, amma an samu wasu dai-daikun mutane da basa kishin kasa na kokarin kawo mata koma baya.

Ya lura da cewa da dama daga cikin adawa da ayyukan hukumar na daga cikin korafe-korafen da aka shigar mata kan sakamakon jarrabawar da dalibai suka rubuta ta shekarar 2019 zuwa 2020 da dai sauran korafe-korafe.

Farfesa Oloyede ya kuma bayyana cewa wadanda ke tuhumar hukumar kan abubuwan da basu kamata ba, basu da wasu kwararan hujjoji da zasu iya dogara da su, wanda hakan ke nuni da cewa marasa kishin cigaban kasa ne musamman ta fuskar ilimi

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!