Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

JAMB:ta kwace lasisin rubuta jarabawa a wasu cibiyoyi goma sha hudu

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da Sakandire ta kasa (JAMB), ta kwace lasisin rubuta jarabawa a wasu cibiyoyi guda goma sha hudu sakamakon masu matsaloli da aka samu musamman tangardar na’urori a cibiyoyin.

 

Shugaban hukumar ta JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci ministan ilimi Malam Adamu Adamu zuwa wasu cibiyoyin rubuta jarabawa da ke birnin tarayya Abuja, don sa ido kan yadda jarabawar gwaji ke gudana.

 

A cewar sa ya zuwa yanzu, cibiyoyi dari shida da casa’in da takwas ne suka ragewa hukumar don gudanar da jarabawar ta JAMB wanda za ayi tsakanin ranakun goma sha daya ga wannan wata zuwa goma sha biyar ga wata.

 

Shugaban hukumar ta JAMB ya kara da cewa, ya zama wajibi su soke lasisin da wasu daga cikin rubuta jarabawar ke da shi sakamakon rashin nagartar su.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!