Labarai
Shugaba Buhari ya ce zai mayar da hankali wajen inganta rayuwar yan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a sabon wa’adin mulkin sa na shekara hudu masu zuwa, zai mayar da hankali ne wajen inganta rayuwar jama’a ta bangare bunkasa ilimi da harkar lafiya.
Shugaban kasar wanda mataimakin sa Farfesa Yemo Osinbajo ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin bikin cikar jami’ar Lagos shekaru hamsin da kafuwa.
Ya ce yaki da fatara da cin hanci da rashawa da samar da aikiyin yi da kuma bin ka’idojin doka na daga cikin bangarori da gwamnati za ta mai da hankali wajen ganin ta kai kasar nan ga tudun mun tsira.
Ya ce gwamnati ta damu matuka kan tafiyar hawainiya da ake samu a bangaren ilimi da harkar lafiya, a don haka ta ga ya zama wajibi ta zage dantse wajen samun nasara a wa’adinta na biyu.
A cewar Farfesa Yemi Osinbajo muhimmancin da harkar samar da abubuwan more rayuwa ke da shi ga ci gaban kowace al’umma, ya sa gwamnati ta dauki gabaran gina sabbin tituna da sabunta wadanda ta gada da shimfida layukan dogo domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan