Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an Hisba sun cafke mata masu zaman kansu

Published

on

Jami’an Hukumar Hisba ta jihar Kano sun sami nasarar cafke wasu mata da maza da ake zargin suna zaman kansu a unguwar na’ibawa da ke yankin karamar hukumar Tarauni a nan Kano.

A cewar hukumar ta samu bayanan sirri ne  cewa, akwai tarin mata da ake zargin masu zaman kansu ne a yankin Na’ibawa ‘yan katako wadanda suka yi sansani a wurin suna cin karensu-babu-babbaka.

Haka kuma hukumar ta ce, a binciken da ta fadada ta kara gano wani sansani a unguwar ja’in layin makabarta da ake zargin shi ma na mata masu zaman kansu har ma hukumar ta yi awon gaba da wani matashi da ya sha barasa ya kuma shiga cikin gidan mata aure yana marisa.

Yayin da Freedom Radio take tattaunawa da matashin bayan ya dawo hayyacinsa ya bayyana cewa matar gidan ce ta kira shi domin ya bata naira 200 za ta sayi fulawa.

Da yake Karin haske kan lamarin, babban darakta a hukumar Dr Aliyu Musa Aliyu ya ce sun sami mata biyu ma masu aure da kuma mata marasa aure a gidan , kuma ya ce za su mika wadanda aka kama din gaban kotu, yayin da  za su nemi kotun da ta basu izinin rufe gidajen.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!