Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shekaru biyar da harin masallacin Kano: Rabon da Liman ya katse Salla fiye da shekaru dari biyar

Published

on

Babban masallacin Kano

YADDA AKA KAI HARI BABBAN MASSALLACIN

A ranar 28 ga watan Nuwambar Shekarar 2014 ne al’ummar jahar Kano suka fuskanci wani mummunan hari da ba’a taba yi ba a tarihin jahar .

Wannan shi ne hari da aka kai babban masallacin Juma’a na jahar Kano lokacin da liman ya kabbara raka’a ta farko a yayin da yake gabatar da sallar juma’a ta wannan rana.

A lokacin da aka kai  harin  al’ummar arewacin Najeriya da ya hada da na yankin arewa maso yamma da na arewa maso gabas su ke fama da harin ‘yan tayar da kayar baya .

Harin da aka kai masallacin juma’ar ta Kano ya yi sanadin asarar rayukan masallata da dama ,wanda ba za’a iya kiyasce yawan su ba.

Harin na masallacin da ke harabar gidan mai martaba sarkin Kano ta wajen kofar kwaru , ya janyo asarar rayukan manya da yara da suka halacci sallar juma’a ta wannan rana.

A lokacin da abun ya faru tarayyar Najeriya na shirin gudanar da babban zaben shekarar 2015 , wanda hakan ya sa ‘’yan siyasa da dama a wannan lokaci su ke  yakin neman zabe , wanda daga bisani su kayi ta tururuwa zuwa jahar Kano domin jajantawa da yin ta’aziyya ga ilahirin al’ummar ta jahar Kano da gwamnati.

Bayan kammala huduba babban liman ya tayar da sallah sai masallata suka fara jin harbe harbe da karar fashewa haka ya sa masallata da liman suka katse sallah suka gudu.

A tsawon na shekaru biyar da harin ya faru, al’umma daga ciki da wajen jahar Kano da ma Duniya baki daya sun jajanta al’amarin harin na bama bamai da aka kawo wa babban masallacin juma’a na farko a birnin na Kano.

Wannan hari dai an kawo shi ne zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda aka zargi gwamnatin sa da yin ko in kula da yaki da ‘’yan tayar da kayar baya.

Harin babban masallacin na birnin Kano ya saka al’umma da dama sun girgiza , wanda hakan ya saka daga wannan lokaci duk wanda zai shiga masallaci a arewacin Najeriya sai an sa wata na’ura an bincike shi.

A ranar juma’ar 28 ga watan Nuwambar ta shekarar 2014 , al’ummar jahar Kano sun rika yin tururuwa zuwa asibitin kwararru na Muratala Muhammad da ke tsakiyar birnin Kano domin bayar da gudunmawar jini ga wadanda suka jikkata a harin.

Sakamakon bayar da gudunmawar ta jinin ya saka hukumomin asibitin na Murtala a wannan lokaci suka bayar da sanarwar cewa jinin da al’umma suka bayar ya ishe su.

 

TAIMAKON AL’UMMA.

A ranar da aka kai harin masallacin  mai martaba sarkin Kano malam Muhammadu Sunusi II bai dade akan karagar sarautar Kano ba ,sai da ya katse ziyarar da yake yi a kasar Faransa ya dawo gida domin alhini da jajantawa al’ummar sa da harin na ya rutsa da su.

Bayan dawowar mai martaba sarkin Kano Muhammadu  Sunusi II , ya shiga masallacin da kansa ya ga irin barnar da harin ya haifar.

Bayan ganewa idanun sa hakan , mai martaba Muhammadu Sunusi II ya  jagoranci salloli biyar a harabar masallacin na juma’a, har ya umarci al’ummar Kano da su gudanar da azumi na wasu ‘’yan kwanaki.

Shi da kansa mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II ya gudanar da azumin ,inda yake jagorantar sallar magariba a  harbar masallacin kuma a sha ruwa tare da shi domin nuna alhini .

Mai martba sarkin Kano Muhammad Sunusi na jagorantar salla a satin harin

Mai martaba sarki Muhammadu Sunusi II ya bayar da gudunmawar fiye da Naira miliyan ashirin ga wadanda harin ya rutsa da su.

Bayan haka shugabanni da kungiyoyi na al’umma sun rika ziyarar jihar Kano ,inda suke zuwa fadar mai martaba Sarki da gidan gwamnatin jahar Kano zamanin injiniya Rabiu Musa Kwankwaso domin bayar da gudunmawar su ta kudade domin taimakawa wadanda suka rasa rayukansu.

WANNE HALI WANDA HARIN YA RUTSA DA SU SUKE CIKI?

Bayan wandanda suka rasa rayukan su a harin bam din na babban masallacin juma’ar na Kano, al’ummar da suka jikkata  ba za’a kiyasce adadin su ba.

Daga cikin wadanda suka jiikkatan da dama daga cikin su sun rasa wasu bangarori na jikin su.

Shekaru biyar kenan da kai harin har yanzu wasu basu warke ba, bayan rashin warkewar ,ko a shekarar bara wasun su sun koka da yadda taimakon da ya kamata a basu bai kai gare suba.

Akwai mata da dama da aka tafi aka bar musu marayu daga daya biyu har zuwa goma sha, Allah madaukakin sarki ne ya san halin da suke ciki.

Shin ko ya zuwa yanzu akwai masu bibiyar lamarin su?

ABIN AL”AJABI

Al’umma da dama musamman ma masu kula da makabartu a jihar Kano sun shaidawa manema labarai a wancan lokaci cewa makabartun birnin Kano da kewaye basu taba karbar al’umma da suka rasa rayukan su kuma ake ta kawo gawawwaki irin na wannan lokaci.

Wasu da manema labarai suka ji ta bakin su a shekarar bara ta 2018, sun ce har a wannan loakci akwai harsasai a jikin su da ba’a cire ba sakamakon rashin abun hannu.

RABON DA LIMAN YA KATSE SALLAR JUMA’A YA GUDU AN KAI SHEKARU FIYE DA DARI BIYAR.

Masana tarihi sun bayyana cewa wannan masallaci da ke kofar Kwaru a harabar fadar mai martaba sarkin Kano, an kai tsawon shekaru fiye da dari biyar liman da mamu basu katse sallar juma’a sun tsere ba, sai a wannan rana ta Juma’a 28 ga watan Nuwambar shekarar ta 2014.

Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya gina wannan masallaci na harabar fadar mai martaba sarki tun a shekarun 1463 zuwa da 99 sanda yana mulkin Kano.

Sauran Sarakuna sun cigaba da habaka wannan masallaci inda sarkin Kano marigayi Abdullahi Bayero da ya mulki Kano daga shekarun 1926 zuwa 1953 ya yi wa wannan masallaci gini na zamani wanda har yanzu shi ne tsarin yadda masallacin yake.

Sai dai bayan harin, Sarkin Kano mai ci a yanzu Muhammadu Sunusi II ya sa an kewaye harabar masallacin sakamakon kai harin da aka yi wanda har izuwa yanzu ba’a san kiyasin mutanan da suka rasu ba.

MENENE MAFITA?

Tunda har ya zuwa yanzu ba’a kai ga gane halin da ake ciki ba game da wadanda suka jikkata, wasu kuma sun nakasa, ya kamata mahukunta da al’ummar gari su bibiyi halin da wadannan al’umma ke ciki domin kafa asusun tallafa musu.

An kafa asusu iri –iri a jahar Kano domin tallafawa wadanda balahira ta shafa kamar konewar kasuwar Sabongari da kuma fito da asusu na tallafawa harkokin ilimi da sauran su.

Me ya kamata a duba game da wadannan bayin Allah da suka riga mu gidan gaskiya da su da iyalansu da kuma wadanda suka daina fita sakamakon nakasa ,lokaci ne kawai zai bayyana hakan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!