Labarai
Jami’an tsaro sun bazama dazukan farautar ‘ƴan bindigar da suka sace dalibai a Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce, wata tawagar sojoji da ‘ƴan sanda da ƴan sa kai sun bazama dazukan da ke yankin domin farautar ‘ƴan bindigar da suka sace ‘ƴan mata fiye da ashirin a wata makarantar kwana a jiya Litinin.
Wani mai magana da yawun gwamnan jihar ya ce gwamnan na tsara wani shiri domin tabbatar da an ceto ƴan matan.
A cewar jami’in biyu daga cikin ‘ƴan matan sun yi nasarar kuɓuta.
Jihar Kebbi dai na samun ƙaruwar hare -haren ‘ƴan bindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa, a baya baya nan.
You must be logged in to post a comment Login