Labarai
Jami’an tsaro sun cafke wadanda ake zargi da kashe-kashe a Filato
Jami’an tsaro a Jihar Filato sun cafke mutanen da ake zargi sun kitsa kashe-kashen kwanan nan a kananan hukumomin Mangu, Bokkos da Barikin Ladi.
’Yan sandan sun cafke mutanen da ake zargi sun kitsa hare-hare da kashe-kashen kwanan nan a kananan hukumomin Mangu, Bokkos da Barikin Ladi na Jihar Filato.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta ce mutum 17 ne suka shiga hannun jami’anta kan harin ranar jajibirin Kirsmetin a kananan hukumomin uku inda aka kashe mutane kimanin 100.
Da yake gabatar da su ga manema labarai, Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da Shiya ta 4, Ebony Eyibio, ya ce tara daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne kan zargin hannunsu a kashe-kashen Mangu, ragowar takwas din kuma kan zargin kashe-kashe a Bokkos d Barikin Ladi.
Eyibio wanda kakakin rundunar, DSP Alabo Alfred, ya wakilta ya ce, “Ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare aka tsegunta mana game da wasu da ke shirin kai hari a yankin Ntam da kuma ASTC da ke Karama Hukumar Mangu, shi ne zaratan jami’anmu suka kai samame suka dakile yunkurin kai harin.
“Hakazalika jami’anmu sun dakile yunkurin masu kona gidaje da wuraren ibada a yankin Panyam da taimakon wasu dattawan yankin.“
You must be logged in to post a comment Login