Labarai
Jami’an tsaro sun daƙile hare-haren da yan Boko Haram suka kai a Maiduguri

Hadin gwiwar jami’an tsaro sun daƙile wasu hare-haren da ake zargin ’yan ta’addar Boko Haram sun kai a yankin Ajilari Cross -Kofa a Maiduguri da kuma Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno a daren wayewar Litinin.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewar jami’an tsaro sun isa yankin Ajilari Cross zuwa Kofa domin duba halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan da suka dace bayan rahoton wani hari da aka dakile.
A wani lamari na daban a Karamar Hukumar Damboa, jami’an tsaro sun dakile wani hari da aka kai da misalin ƙarfe 1 na dare, inda daga bisani aka dawo da zaman lafiya, a yankin.
Haka kuma, Gidan rediyon Dandalkura da ke birnin na Maiduguri ya ruwaito cewa jiragen saman Sojin Najeriya sun kai dauki yayin da aka ji karar harbe-harben bindiga a wasu sassa na birnin Maiduguri, lamarin da ya janyo firgici a tsakanin wasu mazauna yankunan kafin daga bisani lamarin ya lafa.
You must be logged in to post a comment Login