Connect with us

Labarai

Jami’an ‘yan sada sun rufe kofofin shiga majalisun dokokin kasar

Published

on

Jami’an ‘yansada sun rufe kofofin shiga majalisun dokokin kasar nan ta yadda suka hana shiga da fita na ma’aikatan dake a cikin zauren majalisun na kasa.

Jami’an tsaron sun kuma rufe babbar hanyar zuwa dandalin Eagle  Square bayan da suka girki motocin sintiri don hana tashin tarzoma.

Sai dai jami’an  tsaron sun bar manema labarai da ‘yan jaridu da ma’aikatan da suke aikin gine-gine da masu saida kayayyaki shiga cikin majalisar.

Tun a jiya ne dai ma’aikatan dake aiki a cikin majalisar karkashin Kungiyar gamayyar ma’aikata na majalisar suka tsunduma yajin aiki na gargadi na kwanaki 4 don biya musu bukatun su, yayin da suka sanya harkokin majalisar suka tsaya cak.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!