Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da wasu tawagar yan siyasa daga Kano

Published

on

Rahotanni daga fadar shugaban kasa ta Villa na cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da tawagar wasu ‘yan siyasa daga nan Kano da ta kunshi Sanata IsaZarewa da Tsohon mataimakin gwamnan Kano farfesa Hafizu Abubakar.

Mutanen sun je fadar shugaban kasar ne domin tattauna muhimman batutuwan siyasa da kuma yiwuwar sauya shekar su daga jam’iyyar PRP bayan barin su PDP tsagin Kwankwasiyya yanzu kuma zasu koma APC.

Wani makusancin Sanata Isa Zarewa ya tabbatarwa da manema labarai cewar tuni Zarewa ya sanar da sauya  shekar sa daga jam’iyyar PRP zuwa APC bayan ganawar tasu da shugaba Muhammadu Buhari.

Mun kuma tuntubi mai Magana da yawun tsohon mataimakin gwamnan na Kano, Abdulwahab Sa’id inda ya tabbatar mana da cewar farfesa Hafizu Abubakar ya ziyarci Buhari a fadar Villa, kuma ya koma jam’iyyar APC da ya baro a kwanakin baya.

Sauran mutanen dake cikin tawagar  sun hadar da tsohon manajan darakta na hukumar tasoshin jiragen ruwan kasar nan Aminu Dabo da Bala Gwagwarwa da Alhaji Babangida Sulen Garo da Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya daga zagin PDP Kwankwasiyya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!