Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Jami’ar Bayero ta ƙara wa’adin komawar ɗalibai makaranta

Published

on

Jami’ar Bayero da ke Kano ta ƙara wa’adin komawar ɗaliban ta zangon shekarar 2021 da 2022.

Hakan na zuwa ne a lokacin da aka kammala zaman majalisar zartarwar makarantar karo na 392 a ranar laraba, inda aka mayar da komawar ɗaliban a ranar 1 ga watan Nuwambar 2021.

Jami’in yaɗa labarai na jami’ar Malam Lamara Garba ne ya bayyana hakan, a wata sanarwar da jami’ar ta fitar,wanda magatakardar jami’ar Malam Jamilu Ahmad Salim ya sanyawa hannu.

Matakin dai ya biyo bayan rashin sakin sakamakon ɗaliban sakandire na bana.
A baya dai jami’ar ta sanya ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 2021 a matsayin ranar komawar ɗaliban sai dai kuma an ɗage har zuwa 1 ga watan Nuwamba shekarar 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!