Connect with us

Labarai

Jam’iyyar APC bata da ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisu a Rivers da Zamfara

Published

on

Babu ‘yan takaran gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin tarayya na jam’iyyar APC a jihohin Rivers da Zamfara a cikin jerin sunayen wadanda za su tsaya takara ga jam’iyyu daban-daban da hukumar zabe ta kasa INEC ta fitar a jiya Alhamis.

Hukumar ta INEC ta ce tun da fari wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramtawa jam’iyyar APC fitar da ‘yan takara a jihohin Rivers da Zamfara sakamakon rikicin da ya dabai-baye ta a jihohin biyu.

Haka zalika a cikin jerin sunayen mai dauke da sa hannun sakatariyar hukumar ta INEC Rose Oriaran Anthony, babu sunan wanda zai tsayawa jam’iyyar SDP takarar shugaban kasa.

A cewar hukumar ta INEC jam’iyyar ta SDP ba ta da cikakken dan takara sakamakon hukuncin kotu da ta haramta bayyana suna tsohon Gwamnan jihar Rivers Donald Duke a matsayin wanda zai tsayawa jam’iyyar ta SDP takarar shugaban kasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!