Connect with us

Labarai

Dan takarar shugabanci a jami’yyar PDP ya jaddada matsayarsa na sayar da kamfanin NNPC da zarar ya samu nasarar lashe zabe

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya kara jaddada matsayar sa na cewa matukar ya samu nasara a zaben shugaban kasa da za a yi a bana zai sayar da kamfanin mai na kasa NNPC.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a Lagos lokacin da ya ke ganawa da wasu kungiyoyin ‘yan kasuwa a jiya Laraba.

A cewar sa tun yana mataimakin shugaban kasa ya shawarci shugaban kasa na lokacin Olusegun Obasanjo game da sayar da kamfanin na NNPC sai dai ya ki amincewa da sharar sa.

Atiku Abubakar ya ce da an sayar da kamfanin na NNPC tuntuni da yanzu kamfanin ya tsaya da kafar sa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma sha alwashin bunkasa kasafin kudin kasar nan matukar aka zabe shi, yana mai cewar tattalin arzikin Najeriya ka iya kaiwa dala tiriliyan daya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,652 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!