Labarai
Jam’iyyar Labour Party ta ce ba za ta kaurace wa zaben 2027 ba

Jam’iyyar Labour Party ta bayyana cewa ba ta da niyyar kauracewa babban zaben shekarar 2027, sai dai a halin yanzu tana mayar da hankali wajen gyara kura-kuran da suka rage mata ƙarfi a zaben shekarar 2023. Shugabar rikon kwarya ta jam’iyyar, Nenadi Usman ce ta bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a wajen kaddamar da sabon tsarin rajistar mambobi na intanet da jam’iyyar ta yi a Abuja.
Nenadi ta ce kowace jam’iyya tana da matsalolin da suka shafe ta, don haka Labour Party ba za ta bi sahun wasu jam’iyyun da ke barazanar kaurace wa zaben ba. Ta bayyana cewa a zaben 2023 babbar matsalar da suka fuskanta ita ce rashin wakilan jam’iyya a dukkan rumfunan zabe na ƙasar, wanda ya hana su samun takardun hujja da za su gabatar a kotu lokacin da suka kalubalanci sakamakon zaben.
Ta ƙara da cewa yanzu jam’iyyar na ƙoƙarin ƙarfafa ginshikinta a matakin ƙasa, tare da haɗa ƙungiyoyin ma’aikata kamar NLC da Trade TUC domin tabbatar da cewa suna da wakilai a kowane rumfar zabe. A cewarta, wannan zai taimaka wa jam’iyyar wajen tattara sahihan sakamakon zabe da kuma kare hakkinta idan aka samu rikici a zaben 2027.
You must be logged in to post a comment Login