Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jam’iyyar NNPP ta sake sabon tambari

Published

on

Wannan sabon tambarin Jam’iyya da akayiwa take da bunkasa ilimi domin aiwatar da shi a faɗin ƙasar nan, shugabancin jam’iyyar NNPP na ƙasa ya ƙaddamar da wani tambarin sabon jam’iyyar wanda ya kunshi hular digiri, littafi da alkalami wanda akayiwa take da “ilimi ga kowa da kowa. ”

An bayyana wannan tambarin ne da taken taron majalisar zartaswa ta ƙasa na shirye-shiryen taron jam’iyyar na ƙasa da za’a yi a Asabar 6 ga watan Afrilu a babban birnin tarayyar Abuja.

Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta kyawawan manufofin jam’iyyar NNPP waɗanda suka haɗa da samarwa da al’umma ci gaba domin bunƙasa ribar dimokuradiyya.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga magoya bayan jam’iyyar a fadin ƙasar nan da su sake sadaukar da kansu da kuma rike amana da sadaukarwa wajen yada manufofin jam’iyyar a ƙasar nan.

Tun da farko jagoran jam’iyyar na ƙasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya baiwa ɗaukacin ƴaƴan jam’iyyar haɗin kai da yin aiki a matsayin kungiya ta yadda za su ba jam’iyyar goyon baya domin ci gaban jam’iyyar.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna farin cikinsa da jajircewar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir bisa goyon bayan da yake bai wa jam’iyyar tare da bayyana kwarin guiwar cewa Jihar Kano za ta samu sauyi cikin tafiyarsa.

Shugaban riko na jam’iyyar, Dakta Ahmad Ajuji ya ce an samar da majalisar zartaswa ta kasa (NEC) ne domin ta duba ayyukan jam’iyyar kafin babban taron da aka tsara don karfafawa da kuma sanya jam’iyyar cikin kyakkyawan yanayi domin tunkarar kalubalen da ke gabanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!