Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Jam’iyyar PDP ta dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar Arewa

Published

on

Jam’iyyar PDP ta dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar Arewa Sanata. sakamakon zargin wasa da aiki, da kuma cin dunduniyar jam’iyyar.

Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Mr.Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan inda kuma ya ce an kuma dakatar da shi daga kwamitin gudanarwar jam’iyyar.

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar dai ya gudanar da wani taro a ranar biyar ga watan janairun da muke ciki, inda aka yi duba na tsanaki kan zarge-zargen da ake yi masa.

Jam’iyyar PDP dai na fama da matsaloli da suka shafi mambobin su a yankunan arewa maso yammacin da kuma Arewa maso gabashin kasar nan.

Ko da a jiya litinin sai da shugaba Buhari ya karbi wasu kungiyoyin yayan jam’iyyar PDP inda suka yi masa Mubayi’a tare da wasti da jam’iyyar ta PDP.

Anan Kano ma tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kano Injiniya Bello Sani-Gwarzo ya bar jam’iyyar ta PDP tare da shiga jam’iyyar APC.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!