Connect with us

Labarai

Yan sanda sun ceto wata mata mai shekara 80 da aka yi garkuwa da ita

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata tsohuwa mai shekara 80 da aka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke ƙaramar hukumar Minjibir a Kano tare da boye ta a Jigawa.

Mai magana da yawun rundunar SP Lawan Adam Shisu Adam, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa, mutanen da suka yi garkuwa da tsohuwar sun ɓoye ta ne a cikin wani daji na jihar ta Jigawa.

Haka kuma ya ce, bayan sace tsohuwar, barayin sun tafi da ita wasu dazuka da ke tsakanin ƙananan hukumomin Garki da Sule Tankarkar, daga nan ne jami’an rundunar tare da haɗin gwiwar ƴan bijilanti da na ƙungiyar ƴan bulala suka far wa wadanda suka sace ta, inda bayan yin ɗauki-ba-daɗi aka suka samu nasarar ceto ta.

SP Shisu Adam ya ce, jami’an sun yi nasarar kama wasu manyan ƴan fashin daji biyar da aka jima ana nema su ruwa-a-jallo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!