Labarai
Jigawa: Yan sanda sun kama mutanen da ake zargi da satar Mota da Babur

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar cafke wasu da ake zargi da satar mota da kuma babur a karamar hukumar Dutse.
Mai magana da yawun rundunar, SP Shisu Lawan Adam, ne ya tabbatar da hakan a wani saƙon murya da ya raba wa manema labarai da safiyar yau Litinin.
SP Shiisu Lawan Adam ya ce, da zarar sun kammala bincike, za su miƙa waɗanda ake zargi gaban kotu domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su.
You must be logged in to post a comment Login