Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jigawa:mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota

Published

on

Mutum goma sha tara ne suka rasa rayukan su sakamakon wani hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka rasa rayukan su sakamakon hatsarin sun kone, har ta yadda ba’a iya gane fuskokin su, inda wasu suka samu munanan raunuka tare da wani karamin yaro.

A cewar rahotannin karamin ya tsira ne sakamakon cewa mahaifiyar shi yta jefo shi waje daga cikin mkotar, lokacin da ta kwace a hannun direban.

Motar kirar Bus dauke da mutane goma sha takwas da suka taso daga garin Katagun da ke jihar Bauchi, zuwa Ningi, domin halartar bikin aure, ta samu fashewar taya ne a dai-dai lokacin da take tsaka da tafiya, lamarin da ya sanya ta fara dungurawa tare da kamawa da wuta.

 

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar jigawa SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!