Connect with us

Labarai

NYSC:ta karyata cewar masu yi wa kasa hidima zasu karbi alawus din naira 31,800

Published

on

Hukumar dake kula da masu yiwa kasa hidima NYSC ta karyata maganganun dake yawo a kafafan sadarwa na Internet cewa masu yiwa kasa hidima zasu karbi alawus din Naira Dubu Talatin da Daya da Dari Takwas sakamakon sanya hannu kan dokar mafi karancin Albashi da shugaban kasa Muhammadu Buhari yai a satin daya wuce.

Mataimakin Darakta a hukumar ta kasa Eddy Megwa ne ya shaida hakan ga manema labarai jiya a birnin tarayya Abuja da cewa gwamnatin tarayya bata sanya masu yiwa kasa hidimaba a tsarin mafi karancin albashin.

Eddy Megwa ya kuma ce haryanzu masu yiwa kasar hidima za su dinga karbar naira dubu goma sha tara da dari takwas kamar yadda suke karba a duk karshen wata.

Ya kumaja hankalin al’umma da su kaucewa duk wani labari dake yawa a kafofin sadarwa game da hukumar wanda ba itace ta fitar da shiba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!