Labarai
Jihar Kano ce ke kan gaba wajen yawan masu rajistar katin zabe a karon farko – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce, jihar Kano ce kan gaba cikin jihohin da suka fi yawan mutanan da suka kammala rijistar zaben su a kashin farko na shirin da aka fara daga watan Agusta zuwa Disamban nan da muke ciki.
Shugaban hukumar shiyyar Kano Ambasada Abdu A Zango ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Manema Labarai yau Laraba 17 ga watan Disamba 2025.
Shugaban na hukumar INEC shiyyar Kano, ya kuma ce, duk da nasarar da Kano ta samu na yawan wadan da suka yi Rijistar za ta kara fadada cibiyoyin ta musamman a Kananan hukumomin da ke da yawan mutane da kuma nisa.
You must be logged in to post a comment Login