Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kaduna:fulani Igabi sun bukaci da a binciko masu shanun da suka bace a hannun yan sanda

Published

on

Al’ummar Fulani da ke zaune a kauyukan karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna sun yi kira ga kwamishinan yan sandan jihar da kuma gwamnana jihar Nasiru El-Rufa’I da a binciko musu shanun su da suka bace a hannun yan sanda

Fulanin dai sun yi zargi shanun su 31 da tumaki biyu sun salwanta a hannun jami’an yan sandan bayan da jam’an tsaro suka yi awon gaba da su tun a shekarar da ta gabata

Guda daga cikin fulanin mai suna Abubakar Ibrahim ya shaidawa manema labarai cewa, tun da yan sandan suka shiga garin suka yi awon gaba da shanun nasu har yanzu sun kasa samun damar saduwa da dabbobin nasu.

Ya kara da cewa kawo yanzu sun kasha kudaden da yaki miliyna daya da dubu dari bakwai da hamsin domin samun dabbobin nasu amma har yanzu ba amo ba labara

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!