Connect with us

Kiwon Lafiya

Dan takarar jihar Benue karkashin jam’iyyar APC yayi watsi da sakamakon gwamna

Published

on

Dan takarar gwamnan jihar Benue karkashin jam’iyyar APC mista Emmanuel Jime yayi watsi da sakamakon gwamnan da hukumar zaben ta sanar.

A jiya ne dai dan takarar jam’iyyar APC ya yi watsi da sakamakon da hukumar ta INEC ta fitar da ke ayyana gwamna Samual Ortum na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Emanuel Jime ya shaidawa manema labarai cewar ko kadan bai amince da sakamakon ba kuma zai kalubalance shi a gaban kuliya.

A cewar say a zama wajibi ya garzaya kotu domin neman hakkin sa akan gwamna Otom wanda ya zarga da murde zaben da ya gudana.

Ya kuma yi zargin mafiya yawan kuri’un da ake cewa gwamnan ya samu, ya same su ne tas hanyar bankarawa da tursasawa masu zabe su zabi abin da bas hi suke so ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,761 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!