Labarai
Kai tsaye: Kawo yanzu an dai tantance sunaye takwas daga ciki
Kai tsaye: An dai cigaba da tantance kwamishinoni
A halin da ake cikin shugaban majalisar dokoki ya kira Muhammad Sunusi Kiru yayin da fara bayanai kan rauywar sa.
Muhammad Sunusi Kiru dai yayi aiki a ma’aikatar Wasanni ta kasa.
Kuma dan majalisa Sale Ahmed Marke daga mazabar Dawakin Tofa ke masa tamabayoyi.
Kunshin sunayen da gwamnan ya aikewa majalisar dokoki sun hada da:
Engr. Muazu Magaji
Barrister Ibrahim Muktar
Musa Iliyasu Kwankwaso
Dr. Kabiru Ibrahim Getso
Mohammed Garba
Nura Mohammed Dakadai
Shehu Na’Allah kura
Dr. Mohammed Tahir
Dr. Zahara’u Umar
Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa
Sadiq Aminu Wali
Mohammed Bappa Takai
Kabiru Ado Lakwaya
Dr. Mariya Mahmoud Bunkure
Ibrahim Ahmed Karaye
Muktar Ishaq Yakasai
Mahmoud Muhammad
Muhammad Sunusi Saidu
Barrister Lawan Abdullahi Musa
A halin yanzu dai ana tsaka da tantance Ibrahim Ahamed Karaye yayin da aka fara tambayar sa da cea ko ya taba rike mukamin kwamishina.
Wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewa, akasarin tambayoyin da ake wadanda ake tantancewar bai wuce ko sun rike mukamai ba da kuma yadda suke gudanar da ayyukan sub a.
Shugaban majalisar Abdu’aziz Garba Gafasa na dai tantancewar ne da harshen turanci yayin da kuma wasu ‘yan majalisar ke yi musu tambayoyi da harshen Hausa.
Bayan da majalisar ta zauna da misalin karfe tara da minti Arba’in da biyar 45, shugaban majalisar Abdul’azizi Garba Gafasa ya fara kiran sunayen da gwmanan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike musu.
An dai fara da Musa Iliyasu Kwankwaso sai Muhammad Garba sai kuma Murtala Sule Garo.
Harabar majalisar dokoki ta jihar Kano ta dauki harabi biyo bayan sunayen da gwamnatin Kano ta aikewa majalisar a jiya.
Da safiyar yau Talata ne wakilin mu na majalisar dokoki ta jihar Kano Abdullahi Isa ya rawaito cewar an dauke matakan tsaro a ciki da wajen harabar majalisar.
Wakilin na mu ya kara da cewar wadanda aka aike da sunayen na su tuni wasu suka isa harabar majalisar yayin da kuma wasu ke shiga cikin majalisar a halin yanzu.
Ana sa ran nan gaba kadan ne majalisar dokoki ta jihar Kano zata fara zaman tantance kunshin sunayen da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa majalisar a jiya litinin.