Connect with us

Labarai

Kano:Hukumar cin hanci da rashawa ta jihar ta kwato fiye da naira biliyan 4

Published

on

Hukumar Kula da Laifukan Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano ta ce ta kwato fiye da naira biliyan 4 da wasu kadarori daga wajen wasu al’umma da suke yi wa tattalin aziki zagon kasa a jihar Kano a shekaru hudun da suka wuce.

Shugaban hukumar Barista Muhiyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya .

Bari. Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce tun bayan da ya fara aiki a ofishin hukumar ta samu damar sauraron korafai-korafan daga wajen kimanin mutane dubu goma sha hudu, haka nan kuma sun sami wasu sauraron korafai-korafai daga wajen wasu unguwanni guda dubu hudu.

Idan za’a Iya tunawa dai gwamnan Kano Abdullahi umar Ganduje ya nada Muhiyi Magaji Rimin Gado a Yunin  shekara ta 2015 a matsayin shugaban hukumar cin hancin da rashawa ta jihar Kano.

Ayyukan hukumar dai sun hadar da binciken ofisoshin ‘yan siyasa da wasu manyan ma’aikatan gwamnati ba tare da jin tsoro ko fargaba ba kamar yadda Muhuyi Magajin ke bayyanawa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,906 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!