Labarai
Kai tsaye: An Kammala tantance Baba Impossible
Yayin da ake tantance shugaban kwamitin sake yin nazari kan karantun Almajiranci da na tsangayu Baba Impossible, yace lokacin da yake rike da mukamin shugaban hukumar ilimi mai zurfi ya kawo sauye-sauye.
A cewar, Babba Impossible ya rike ma’aikatar ne na watanni hudu kuma yayi kokarin ganin an biya kudin tallafin karatu na dalibai na cikin gida da na ketare.
An dai tantance Shehu Na’Allah Kura wanda wasu daga cikin ‘yan majalisar suka yi masa tambayoyi kan yadda ya gudanar da aikin sa yana kwamshinan kasafin kudi da tsare-tsare.
Shehu Na’Allah Kura ya bayyana cewar, ya gaggauta aiwatar da kasafin kudin bara kan lokaci.
Bayan da aka tantance tsohun kwamishinan shari’a sai kuma tsohun kwamishinan lafiya Dr, Kabiru Ibrahim Getso wanda yake amsa tambayoyin ‘yan majalisar.
Dr, Kabiru Ibrahim Getso dai ya fara da amsa tambayar irin cigaban da ya kawo a gwamnatin Ganduje a wa’adin sa na farko.
wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewar, Kabiru Ibrahim Getso na cewa ya kawo cigaba da suka hada da nada linkafar wasu jami’an kiwon lafiya da samar da sabbin asibitoci da dai sauran su.
A halin da ake cikin ana tsaka da tantance tsohun kwamishinan shari’a Barrister Ibrahim Muktar yayin da ya bayyana irin cigaban da ya kawo a zangon farko na gwamnatin Ganduje.
An dai kammala tantance tsohuwar mataimakiyar kwamandan Hisbah Dr, Zara’u Muhammad Umar.