Connect with us

Labarai

Kai tsaye: Ana saran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iso Kano daga yanzu

Published

on

Shirye-shirye sun rigaya sun kammala don  tarban shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen yaye daliban da suka karbi horo a kwalelejin horars da ‘yan sanda ta jihar Kano.

Tuni dai sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya isa harbar kwalejin yayin da kuma sabbin masarautun yanka hudu suma suka isa wajen.

Ana dai sa ran cewa za’a yaye jami’an ‘yan sanda dari shida da Ashirin da takwas da suka karbi horo a kwalejin.

Kazalika gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano don tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari

Wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewar, an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen kwalejin yayin da ake dakon shugaban kasa Muhammadu Buhari don fara taron.

Yanzu haka tuni komai ya gama kankama ana jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bikin yaye ‘yan sanda a jami’ar ‘yan sanda ta kasa da ke garin Wudil ana Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!