Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kai tsaye: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jami’ar horar da ‘yan sada a nan Kano

Published

on

A halin da ake ciki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa harabar jami’ar horar da jami’an ‘yan sanda dake garin Wudil anan Kano.

Wakilan Freedom  Radiyo sun rawaito cewar tuni aka fara taken Najeriya bayan da shugaban kasa ya isa wajen.

Za’a iya bibiyar mu kai tsaye ta shafin mu na facebook don ganin yadda taron ke wakana kai tsaye.

Shirye-shirye sun rigaya sun kammala don  tarban shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen yaye daliban da suka karbi horo a kwalelejin horars da ‘yan sanda ta jihar Kano.

Tuni dai sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya isa harbar kwalejin yayin da kuma sabbin masarautun yanka hudu suma suka isa wajen.

Ana dai sa ran cewa za’a yaye jami’an ‘yan sanda dari shida da Ashirin da takwas da suka karbi horo a kwalejin.

Kazalika gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano don tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari

Wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewar, an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen kwalejin yayin da ake dakon shugaban kasa Muhammadu Buhari don fara taron.

Yanzu haka tuni komai ya gama kankama ana jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bikin yaye ‘yan sanda a jami’ar ‘yan sanda ta kasa da ke garin Wudil ana Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!