Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai tsaye : Sarkin Kano na karbar tawagar masu zuba jari daga kasar China

Published

on

A yanzu dai a na tsaka da cin abinci bayan da Hakiman sarki su kamala gaisuwa yayin da mai martaba sarkin Kano ke cigaba da karbar tawagar yan kasar Sin masu son zuba jari a kasar nan a fadar dake Kofar Kudu.

A halin yanzu maimartaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II ya zauna a fadarsa yayinda yake karbar bakunci tawagar masu sanya hannun jari daga kasar China don bunkasa jihar Kano a fadarsa.

Ku cigaba da bibiyarmu kai tsaye ta shafin mu na Facebook a Freedom Radio Nigeri

Maimartaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II na karbar bakuncin rukunin masu zuba jari daga kasar China yau jumu’a a fadarsa.

Idan zaku iya tunawa dai a baya-bayan nan ne gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da maimartaba sarkin suka gana da ‘yan kasuwar a birnin legas, domin lalubo hanyoyi da zasu sanya hannun jari don bunkasa al’amura a jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan ziyarar da maimartaba sarkin ya kai kasar China kan yadda za’a bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Ku cigaba da bibiyarmu kai tsaye ta shafin mu na Facebook a Freedom Radio Nigeria, kallon yadda take wakana a kai tsaye a fadar mai martaba sarkin Kano

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!