Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mahukunta su mai da hankali kan al’umma -Limami

Published

on

Babban limamin massalacin juma’a na tokarawa Malam Ado Ya’u ya ce shuwagabanin kananan hukumomi su  mai da hankali a kan al’ummar da suke jagoranta a nan jihar kano.

Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da taron wayar da kan matasan garin  na Tokarawa dake karamar hukumar Nassarawa.

Malam Ado Ya’u ya kara da cewa matasan garin  Tokarawa suna fama matsalar makarantar firamare da sakandare da kuma matsalar wutar lantarki.

Matasan garin   suna kira da  shugaban karamar hukumar nassarawa ya tallafamusu da kayayyakin more rayuwa kasancewar ta hakan ne za su sami cigaba.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa malamai da dattawa da matasa suna kira da Gwamnatin jihar kano data kawo musu dauki a garin nasu ta tokarawa.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!