Connect with us

Labarai

A karon farko jarumai Hrethik Roshan da Akshey Kumar zasu fito tare a cikin film

Published

on

Daga

A cikin wani sabon rahoto da shafin Firmfare dake kasar India ya fitar ya nuna cewa ana saran manyan jaruman biyu zasu iya fitowa tare a cikin wani sabon shiri wanda ba’a bayyana sunansa ba.

Wadannan manyan jarumai guda biyu a tarihin fara fina finansu a masana’antar shirya fina finai ta Bollywood dake kasar India basu taba haduwa tare ba a firm, kasancewar duk jaruman suna takama da nasarar da fina finansu ke samu da zarar sun fita.

A cikin shekarar da mukayi bankwana da ita ta 2019 jarumi Akshey Kumar ya fitarda sabbin fina finai har guda Hudu, wanda ake ganin babu wani jarumi a shekarar 2019 a masana’antar shirya fina finai ta Bollywood da fina finansa suka sami irin nasarar da fina finan sa suka samu.

Haka zalika a shekarar da mukayi bankwana da ita shima jarumi Hrethik Roshan ya fitarda sabbin fina finansa har guda biyu kuma shima sunyi matukar yin kasuwa.

Sai dai a cikin wannan sabon firm din da ake saran jaruman biyu zasu fito tare a cikinsa wanda ba’a bayyana sunan firm din ba zuwa yanzu , ana saran shima Jarumi Rana Daggubati zai fito a cikin firm din.

Sai dai babban abun tambayar nan shine wadannan manyan jarumai guda biyu Akshey Kumar da Jarumi Hrethik Roshan kowannansu yana aikin wani firm din a halin yanzu.

Rubutu daga

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!