Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Kamfanonin Jiragen Sama sun koka bisa hauhawar farashin man Jiragen

Published

on

Ma’aikatan Jiragen sama sun nuna damuwarsu kan cigaba da samun hauhawar farashin man Jirgi wato Jet A1.

A yanzu haka dai farashin man ya kai naira 315 a duk lita daya, lamarin da ya sanya wani kwararren masanin harkokin Jiragen sama ya ce, ka iya kawo karin kudin Jirgi a Najeriya.

Ya kuma ce, a yanzu ana sayar da tikitin sa’a daya daga kan kudi naira dubu 45 zuwa naira dubu 60 musamman idan akwai karancin fasinjoji.

Daga shekarar 2016 farashin litar man ya karu da kaso 200, inda ya tashi daga naira 160 zuwa naira 305 a farkon wannan shekarar da muke ciki, yayin da kuma ya kai naira 315 a karshen makon da ya gabata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!