Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ta gaza cimma matsaya da kungiyar likitoci masu neman kwarewa

Published

on

Gwamnatin tarayya ta gaza cimma yarjejeniya tsakaninta da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa NARD domin kawo karshen yajin aikin da suke yi.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala zaman taron, shugaban kungiyar Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi ya ce ya zuwa yanzu babu wata matsaya da kungiyar ta cimma da gwamnatin tarayya.

To sai dai ya ce za su ci gaba da tattaunawa a yau Talata 10 ga watan Augusta don samar da sulhu a tsakani.

Dr. Uyilawa ya ce yanzu haka kwamitin lafiya na majalisar wakilai yana gudanar da wani taro da ma’aikakatar lafiya da kuma wakilan kungiyar domin cimma matsaya.

Ya kuma ce gwamnatin tarayya na rokon su domin komawa bakin aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!