Connect with us

Labarai

Kano: Ƴan sanda sun cafke mai buga jabun takardun ɗaukar aiki

Published

on

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta kama wani mutum da ya kware wajen buga takardun daukar aiki na bogi.

Mutumin mai suna Rabi’u Sani mazaunin karamar hukumar Dala mai shekara 62 ya amsa laifin da ake zarginsa da shi a gaban rundunar Yan sandan.

Ya ce shi da abokan su 3 sun dade suna wannan sana’a ta buga takardun daukar aiki na bogi suna sayarwa ga masu neman aiki.

Da yake bayanin yadda wannan gurbatacciyar sana’ar tasu take, Rabi’u Sani ya ce masu neman aiki a ma’aikatar ilimi suke siyarwa da takardar, tare da karbar kudi da ya kama daga dubu 40 zuwa 60.

Mai magana da yawun rundunar Yan sandan jihar Kano DSP Abdullah Haruna Kiyawa ya ce sun sami korafi daga wata mata wadda ya karbi kudinta ya bata takardar ta bogi tsahon watanni biyar ba tare da ta ga albashi ba.

Abdullahi Kiyawa ya ce sun sami mai laifin da takardar bogin guda 30 tare da kudi kimanin miliyan 3 da dubu dari takwas a hannunsa baya ga wasu kudaden kimanin miliyan daya da dubu dari biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!