Labarai
Kano: Ƴan bindiga sun kai hari garin Minjibir
Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki garin Minjibir da ke Kano inda suka ƙone motar ƴan sanda tare da sace wani attajiri.
Wani mazaunin garin ya shaida wa Freedom Radio cewa, ƴan bindigar sun shiga garin da misalin ƙarfe 2 na dare.
Ƴan bindigar sun fara harbe-harbe a unguwar Amsharu da ke garin, ko da ƴan sanda suka yi musu martani sai aka shiga bata-kashi.
A cewarsa, ƴan bindigar sun ƙone motar ƴan sandan tare da sace wani attajiri Alhaji Abdullahi Kalos.
Koda muka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna ya ce, bai samu rahoton ba amma zai bincika.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da ƴan bindigar suka sace matar wani attajiri sannan suka ƙone motar ƴan sintiri a garin Falgore na ƙaramar Rogo.
You must be logged in to post a comment Login