Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: ASUU ta janye yajin aiki

Published

on

Kungiyar malaman jami’o’I a Najeriya ASUU, ta janye yajin aikin da ta dauki tsawon watanni tara tana yi.

Shugaban kungiyar a kasar, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya sanar da hakan a wani taron gaggawa da kungiyar ta shirya a Abuja.

Farfesa Biodun, ya ce janye yajin aikin na zuwa ne bayan tattaunawa da suka yi da majalisar zartaswar kungiyar.

A ranar Talata ne kungiyar malaman jami’o’in ta yi zaman tattaunawa da ministan kwadagon kasar Chris Ngige, domin cimma matsaya kan bukatun bangarorin biyu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!