Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kano: An kama mai safarar mutane a filin jirgi

Published

on

Da safiyar yau ne jami’an tsaron filin jirgin saman Malam Aminu da ke nan Kano suka cafke wata mata mai matsakaicin shekaru dauke da jariri dan wata shida da ake kyautata zaton sato shi ta yi.

Jami’an sun kama matar dai-dai lokacin da za ta hau jirgin don zuwa Jihar Lagos.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa manema labarai cewa tuni aka mika matar ofishin ‘yan sanda na filin Jirgin saman Malam Aminu Kano don fadada bincike domin daukar matakin da ya dace a kai.

Ko da muka kira jami’ar hulda da jama’a ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano Maimuna Tadafe don karin haske kan batun ba ta amsa wayarmu ba, kuma ba ta magantu ba kan sakon kar ta kwana da aka tura mata.

A ‘yan kwanakin nan dai ana ta samun damar ceto kananan yara da ake sacewa daga jihohin Arewacin Najeriya ana sayar da su jihohin kudancin kasar.

Ko a cikin watan Oktoban da ya gabata an ceto wasu yara 9 ‘yan asalin Kano da aka sace aka kuma sayar da su a jihar Anambra inda aka mayar da su Kiristoci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!