Labarai
Kano: An kama miyagun kwayoyin na miliyan 150
Gwamantin jihar kano ta ce jami’anta sun kama katan145 na magungunan da wa’adinsu ya kare hadi da miyagun kwayoyi boye a wani wurin ajiyar kayayyaki a Nijar road dake yankin Sabon Gari a karamar hukumar Fagge.
Kwamshinan lafiya Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana haka a yau Alhamis jin adan bayan kama miyagun kwayoyin da aka yi , da hadin gwiwar kwamitin bincike kan miyagun kwayoyi, da hukumar NAFDAC.
Kwamishinan wanda daraktan kula da magunguna kuma shugaban kwamitin na ma’aikatar ya wakilce shi Abdu Umar Madaki, ya kara da cewa daga cikin magungunan da suka kama akwai magungunan masu fama da ciwon suga, da vitamins da wasu magungunan da suka kai na kimanin naira miliyan 150.
Ya ce kwamitin zai cigaba da hada kai da dukkannin hukumomin da suka dace wajen tabbatar da an kawo karshen jabun magunguna da ke zagawa birni da kauyukan jihar Kano.
Abdu Umar ya kuma ce tuni kwamitin ya tabbatar da wanda yake da alhakin boye magungunan a gidan ajiye kayayyakin aka kuma mika shi ga hukumomi domin hukunta shi.
Haka kuma ya bukaci masu ruwa da tsaki da su taimaka wa gwamnati wajen magance matsaloli tare da kai karar kwayoyin da wa’adinsu ya kare har ma da miyagun kwayoyi ga hukumomin da suka dace, domin daukar matakin gaggauwa.