Labarai
Kano: An yi jana’izar mutanen da suka rasu sakamakon fadan Daba
An gudanar da zana’izar wasu mutane biyu da suka rasa ransu a daren jiya Lahadi sakamakon faɗan daba a yankin unguwannin Yakasai da Rimi da Kofar Mata da kuma Zage.
Rahotonni sun bayyana cewa, a daren jiya ne wasu bata garin matasa suka farmaki mutane sakamakon fadan daba da suka tayar.
Sai dai har zuwa safiyar yau Litinin mazauna yankin Yakasai na zaman ɗar-ɗar sakamakon yadda faɗan daban ya sake tashi.
Freedom Radio ta kai ziyar ganin da ido da safiyar Litinin din nan inda ta tattauna da wasu mazauna yankin inda suka bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga kallon kwallon kafa a filin wasa na Kofar Mata.
You must be logged in to post a comment Login