Labarai
Kano ce kan gaba wajen yaki da cin hanci da rashawa- Gwamna
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ‘jihar Kano ce kan gaba wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar nan’.
Abba Yusuf ya bayyana haka ne a wajen bude taron kwana guda na yaki da cin hanci da rashawa kan rawar da jami’an tsaro ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tare da rundunar ‘yan sandan jihar ne suka shirya taron bitar a cibiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano a yau Alhamis.
Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Dr Abdullahi Baffa Bichi ya wakilta ya ce gwamnatin ba ta tsoma baki a harkokin hukumar.
Wanda ya Kara da cewa ‘gwamnati mai ci ta gaji dimbin laifukan da ake zargi na cin hanci da rashawa daga gwamnatin da ta shude a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje’.
Yusuf ya ce taron zai inganta hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da Hukumar, yana mai cewa, “an yi shi ne don ganin an aiwatar da dokokin hukumar baki daya.”
Ya ce ‘Kotun ta ce hukumar na da hurumin binciken duk wata almundahana da ake zargin a jihar.” Ya kara da cewa’.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Muhyi Magaji rimin gado, ya ce ‘makasudin gudanar da taron shi ne inganta hadin gwiwa tsakanin hukumar da jami’an tsaro domin cimma manufofin da aka sanya a gaba’.
Wanda ya sha alwashin cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a jihar.
Tun da farko, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Usaini Muhammad Gumel, ya ce rundunar ‘yan sandan da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da baiwa hukumar goyon bayan da ya dace domin karfafa yaki da cin hanci da rashawa.
You must be logged in to post a comment Login