Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya ja hankalin jami’an tsaro kan karbar na goro

Published

on

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira da al’ummar kasar nan dasu daina bawa jami’an tsaro na goro.

Sarkin ya bayyana haka ne a wajen taron da hukumar yan sanda da hadin gwiwar hukumar karbar korafe korafe ta jahar kano ta Anti Corruption suka shirya don samar dasu hanyoyin da za’a wajen magance cin hanci a jahar nan.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace ya gamsu da yunkurin da hukumar karbar korafe korafe tare da hadin gwiwar jami’an tsaro wajen yaki da cin hanci da rashawa a jahar nan dama kasa Baki daya.

A nasa jawabin shugaban hukumar karbar korafe korafe ta jahar kano Muyi Magaji Rimin Gado yace ‘sun shirya wannan taron domin su zaburan da jami’an tsaro akan yanda za’a magance cin hanci da rashawa a kasar nan’.

Freedom Radio ta rawaito cewa taron ya mai da hankali ne akan yanda za’a magance cin hanci da rashawa a jahar dama kasa baki daya.

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!